in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na son ci gaba da inganta goyon bayan ayyukan kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa
2014-09-10 21:35:35 cri
Ranar 10 ga wata, Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, kasar Sin na son ci gaba da inganta goyon bayan ayyukan kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa, ciki had da tura sojojin kasar don su shiga rundunar musamman da MDD ta aika zuwa kasar Sudan ta Kudu. Yanzu kasar Sin na tuntubar sakatariyar MDD yadda ya kamata.

Madam Hua ta kuma kara da cewa, har kullum kasar Sin na shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD cikin himma. Makasudin kasar Sin na shiga wadannan ayyuka shi ne sauke nauyin da MDD ta dora mata a tsanake wajen warware rikici cikin ruwan sanyi, kara azama kan bunkasuwa da farfadowa da kiyaye zaman lafiya da tsaro a shiyya-shiyya. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China