in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da babban taron MDD karo na 69
2014-09-17 15:32:42 cri
An kaddamar da babban taron MDD karo na 69 a cibiyar MDD dake birnin New York a ranar 16 ga wata.

Shugaban babban taron a wannan karo daga kasar Uganda Sam Kutesa ne ya sanar da bude taron. A jawabin da ya gabatar Kutesa ya yi kira ga kasashe mambobin MDD da su yi amfani da dandalin MDD wajen lalubo hanyoyin warware matsalolin dake addabar Bil'adama.

A yayin taron na bana, ana sa ran shuwagabannin kasashe da na gwamnatoci fiye da 140 za su yi muhawara, kana a gudanar da taruka kan batutuwan sauye-sauyen yanayi, da yaki da cutar Ebola da dai sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China