Bugu da kari, an jaddada cikin kudurin cewa, ya kamata bangarori daban daban da rikice-rikicen ke shafa su girmama ayyukan ma'aikatan jin kai da ma'aikatan MDD tare da kuma kiyaye tsaronsu, an kuma yi allah wadai da dukkanin hare-hare ko barazana da aka kai ga ma'aikatan jin kai, haka kuma, cikin kudurin, an yi kira ga bangarori daban daban da rikice-rikicen ke shafa su taimakawa ma'aikatan jin kai da su gudanar da ayyukan samar da agaji cikin 'yanci.
A cikin kudurin kuma da kwamitin sulhu na MDD ya fitar, an ce, kwamitin zai dauki matakai da dama don tabbatar da tsaron ma'aikatan jin kai.
Haka kuma, shugaban kwamiti na watan, zaunannen wakilin kasar Burtaniya dake MDD Mark Lyall Grant ya bayyana wa kafofin watsa labaran cewa, wannan shi ne karo na farko da aka zartas da wani kudurin kiyaye tsaron ma'aikatan jin kai a kwamitin sulhu na MDD, bayan da aka kai hari ga ofishin MDD dake birnin Baghdad na kasar Iraq a shekarar 2003. Cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, ma'aikatan jin kai sun sha fama da hare-haren da aka kai musu yayin da suke gudanar da ayyukansu, wadanda suka haddasa mutuwar ma'aikata 79 a shekarar bana. (Maryam)