in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu nasarar tseratar da ma'aikatan wanzar da zaman lafiyar MDD
2014-08-31 16:14:24 cri
Ofishin MDD ya ce an samu nasarar kara kubutar da wasu ma'aikatan wanzar da zaman lafiya 'yan asalin kasar Philippine su 40 daga hannun mayakan Islama, bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da mayakan a wani wuri dake tuddan Golan.

Wani mai magana da yawun MDDr ya shaidawa 'yan jaridu cewa ya zuwa yanzu akwai ma'aikatan tawagar wanzar da zaman lafiya fiye da 70 da aka kubutar, suke kuma wani wuri mai samun kariyar jami'an tsaro.

A ranar Asabar ne dai wata tawagar MDD mai kunshe da dakarun musamman ta UNDOF ta samu nasarar kubutar da wasu ma'aikatan su 32, an kuma ce jami'an sun samu kubuta ba tare da samun koda kwarzane ba.

Sai dai a daya hannun, kakakin MDDr ya ce har ya zuwa yanzu akwai wasu ma'aikatan wanzar da zaman lafiyar MDDr su 44, dake hannun mayaka 'yan gwagwarmayar kasar Sham.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China