in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin kawar da wariyar launin fata na MDD ya nuna damuwa kan munanan matakan da 'yan sandan Amurka suke dauka
2014-08-30 17:14:55 cri
Jiya Jumma'a 29 ga wata, kwamitin kawar da wariyar launin fata na MDD ya samar da sakamakon bincikensa kan rahoton da kasar Amurka ta gabatar game da yadda take gudanar da yarjejeniyar kawar da wariyar launin fata ta kasa da kasa, inda kwamitin ya nuna damuwarsa matuka kan munanan matakan da 'yan sandan Amurka suke dauka yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Kwamitin ya nuna yabo dangane da kokarin da kasar Amurka ta yi kan aikin kawar da wariyar launin fata a kasar, amma ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, al'amuran wariyar launin fata na ci gaba da kasancewa cikin zaman takewar al'ummar kasar Amurka.

Dalilin haka, kwamitin ya yi kira ga hukumomin kasar Amurka da abin ya shafa da su gudanar da bincike yadda ya kamata kan daukacin munanan matakan da 'yan sandan kasar Amurka suka dauka yayin da suke gudanar da ayyukansu, domin hukunta masu laifin yadda ya kamata da kuma ba da diyya ga mutanen da lamarin ya shafa ko iyalansu. Bugu da kari, ya kamata a dauki matakan da za su dace wajen warware matsalar tun daga tushe, ta yadda za a iya kawar da irin wanann lamari a kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China