Wasu sojojin uku na MDD sun samu rauni a yayin da wata motarsu ta taka nakiya da aka dasa a kan hanya.
Wannan harin ya faru kusa da wani kauyen Aguelhok dake yankin Kidal, adadin ya kai zuwa 21 sojojin MDD da aka kashe sannan sojojin wanzar zaman lafiya 84 suka jikkata sakamakon fashewar boma bomai a kasar Mali, tun fara aikin wannan tawaga a ranar daya ga watan Julin shekarar 2013.
A cikin wata sanarwa zuwa ga manema labarai da kakakinsa ya gabatar, Ban Ki-moon yayi kira ga kungiyoyi masu makamai dake taro a birnin Alger da su gaggawata gaggauta aiwatar da niyyar da suka dauka cikin wata sanarwarsu na yin aiki tare da tawagar MINUSMA domin kawo karshen hare hare kamar da yadda yarjejeniyar ranar 16 ga watan Satumba ta tanada. Ya kamata a kawo karshen wadannan hare hare kan sojojin MDD ba tare da bata lokaci ba in ji kakakin Ban Ki -moon. (Maman Ada)