Wakilai daga kasashe, yankuna da kungiyoyin duniya kusan 21 suka halarci wani taron kasa da kasa game da batun tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa a kasar Libya a ranar 17 ga wata a birnin Madrid, inda firaminstan kasar Sifaniya Gobierno Rajoy ya yi kira da a kafa wata kasar Libya mai ikon kanta, inda ake samun hadin kan al'umma, da wadata, gami da tsarin demokuradiyya.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Libya Mohamed Abdel-Aziz ya bayyana cewa, kasarsa ta Libya ba ta da cikakken karfi wajen tinkarar kalubalen da take fuskanta, don haka tilas ne gamayyar kasa da kasa ta taimaka wajen yaki da kungiyoyin ta'addanci da kuma yanke hukunci kansu. Kana kamata ya yi kasa da kasa su dauki matakai don hana 'yan ta'adda na wasu kasashe shiga kasar Libya. (Zainab)