A yayin taron maneman labaran da aka yi bayan taron, shugaban kwamitin harkokin sojan kungiyar NATO Knud Bartels ya bayyana cewa, abubuwan da aka tattauna a yayin taron sun hada da batutuwan kasashen Rasha, Ukraine da na yankunan Sahel, Gabas ta Tsakiya, Afirka ta arewa da kuma Asian-Pacific.
Ya kuma kara da cewa, babban batun da aka tattauna a yayin taron shi ne, yadda za a iya ciyar da shirin kafuwar wata rundunar sojojin ta matakin share fage, ya ce, kungiyar NATO ta iya tura sojoji da kayayyakin soja a wuraren dake bukata cikin gajeran lokaci.
Yayin da yake tsokaci kan batun Afghanistan, Mr. Bartels ya bayyana cewa, kungiyar NATO za ta samar da horaswa ga sojojin kasar Afghanistan bayan ta janye sojojinta daga yankin.
Ko wace shekara, kwamitin harkokin sojan kungiyar NATO na gudanar da tarukan manyan hafsoshin kungiyar sau uku, biyu daga cikinsu ana yin su a birnin Brussels, dayan kuma ana yinsa a tsakiyar watan Satumba a wata mambar kasa ta kungiyar. (Maryam)