in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar NATO ta gabatar da shirin habaka
2014-09-06 16:58:57 cri
Anders Rasmussen, babban magatakardan kungiyar tsaro ta NATO, ya sanar a ranar 5 ga wata cewa, kungiyarsa za ta kara nuna sassaucin ra'ayi da kokarin hadin gwiwa da bangarori daban daban, don cimma burin da ta sanya a nan gaba, ta yadda za a samu damar shawo kan barazanar da ake gamuwa da ita a wannan zamani yayin da ake kasancewa cikin wani sabon yanayi. Haka kuma jami'in ya ce a shekaru 10 masu zuwa kungiyar NATO za ta kara zuba jari don raya fasahohin soja, lamarin da ya sanya mutane dubbai masu adawa da yunkurin yaki, suka yi zanga-zanga don nuna kin amincewar su kan habakar kungiyar NATO.

Rasmussen ya bayyana hakan ne a taron manema labaru da aka kira bayan wani taron majalisar gudanarwa ta NATO, inda aka sanar da shirin musamman na share fagen abkuwar yaki, da alkawarin kafa wata rundunar wadda za ta iya mayar da martani inda yaki ya barke nan take. Ta wannan sabon shirin da aka tsara, ana sa ran ganin kungiyar NATO ta kula da matsalolin da ke kawo barazana ga tsaronta cikin sauki, ta yadda za a samu damar ba da kariya ga dukkan kasashe mambobinta.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China