in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NATO ta kammala aikin girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami a kasar Turkiya
2013-02-17 15:51:08 cri

Kungiyar NATO ta ba da wata sanarwa a ran 16 ga watan nan cewa, yanzu haka ta kammala aikin girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami guda shida a kasar Turkiya, wadanda za a iya amfani da su nan da nan. Ban da haka, kungiyar ta jaddada cewa, ita ce ke mallakar wadannan na'urori.

Sanarwar ta kara da cewa, an girke na'urar karshe ne a ran 15 ga wata, kuma Amurka ce ta samar da ita, wadda kuma ita ce aka sanya a birnin Gaziantep, a kudu maso gabashin kasar Turkiya, duka dai da zummar karfafa tasirin kasar, wajen tabbatar da tsaron sararin samaniyarta, da kare jama'arta, dama yankunanta gaba daya, ta yadda za a kare yaduwar rikicin daka iya tsallakawa iyakar kasar.

Idan za a iya tunawa, a ran 4 ga watan Disambar bara ne, taron ministocin wajen NATO ya amince da rokon da Turkiya ta yi, na girke wadannan na'urori a kan iyakarta, domin kiyaye harin makamai masu linzami da kasar Sham za ta iya kai mata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China