A cikin sanarwar karfin kiyaye tsaro ta taron koli na kungiyar tsaron NATO da aka bayar a karshen taron, an ce, dalilin rashin isashshen kudi a fannin harkokin tsaro, shugabannin kungiyar tsaron NATO sun tsaida kudurin dora muhimmanci kan manufar kiyaye tsaro ta hanyar da ta dace, da kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe membobin kungiyar a wannan fanni don cimma burin tabbatar da inganta karfin soja zuwa shekarar 2020.
A gun taron, shugabannin kungiyar tsaron NATO sun jaddada muhimmancin kafa tsarin kiyaye tsaro mai inganci a nahiyar Turai, kana an bayyana nasarorin da aka samu kan mataki na farko na tsarin kiyaye tsaro ta hanyar makamai masu linzami na nahiyar Turai.
Ban da wannan kuma, an gudanar da taron musamman game da batun kasar Afghanistan, inda aka bada shawarwari kan makomar kasar bayan shekarar 2014. Bayan da sojojin bada gudummawa na kasa da kasa suka mika dukkan ayyukan kiyaye tsaro ga sojojin kasar Afghanistan kafin karshen shekarar 2014, kungiyar tsaron NATO za ta taka rawar bada horaswa da taimako a madadin yin yaki a kasar.(Zainab)