A wannan rana, kwamitin tsaida kuduri na kungiyar tsaro ta NATO ya shirya taron jakadun kasashen waje da ke kasar Turkiyya bisa bukatun kasar, inda aka tattauna batun harbo jirgin saman yaki na Turkiyya da Siriya ta yi. A cikin sanarwar da Rasmusen ya bayar bayan taron, an ce, ba za a amince da harbo jirgin saman yaki na kasar Turkiyya ba, kuma ya yi Allah wadai da wannan batu da kakkausan harshe. Ya ce, kungiyar tsaro ta NATO za ta ci gaba da mai da hankali game da batun.(Bako)