Da yake bude taron, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya nuna cewa NATO ta kasance wani ginshikin tsaron hadin gwiwa na kasashen mambobinta.
Obama ya bayyana cewa kasashen kungiyar za su kara dukufa a cikin sabbin ayyukan tabbatar da kwarewa domin fuskantar sabbin kalubalen tsaro.
Kasashe mambobin NATO ya kamata su kara yin hadin gwiwa tare da kasashe makwabtansu da kuma abokan hulda domin karfafa yanar gizo ta hadin gwiwa a duniya a fannin tsaro.
Sakataren janar kungiyar NATO, Anders Fogh Rasmussen ya bayyana a nasa bangare cewa taron zai sake sabunta niyyarsa ta dangantaka mai alfanu tsakanin Amurka ta arewa da kasashen tarayyar Turai a wannan karni na 21. ( Maman Ada)