in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma matsaya daya a fannoni da dama a gun taron koli na kungiyar NATO da aka yi a birnin Chicago
2012-05-22 16:37:18 cri

An rufe taron koli na kungiyar NATO a karo na 25 a ran 21 ga wata da yamma wanda aka shafe kwanaki 2 ana yin sa a birnin Chicago na kasar Amurka, kuma an cimma matsaya daya a fannoni da dama kan batutuwan kara karfin sojojin kungiyar NATO da batun Afghanistan.

Sanarwar karshen taron da aka fitar ta bayyana cewa, a wannan lokaci da ake fama da karancin kudi, shugabannin kungiyar NATO sun yanke shawarar karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashe membobin kungiyar domin cimma burin kara karfin aikin soja kafin shekarar 2020.

Bugu da kari, shugabannin NATO sun jaddada muhimmancin kafa tsarin tsaro mai inganci a nahiyar Turai, kuma sun gabatar da sakamakon da aka samu wajen matakin farko na kafa tsarin kandagarkin makamai masu linzami.

Game da batun Afghanistan, kungiyar NATO, ta yi hasashen makomar kasar Afghanistan bayan shekarar 2014. Kuma sojojin kasa da kasa zasu mika ikon kiyaye tsaro ga rundunar sojojin kasar Afghanistan kafin karshen shekarar 2014, amma kungiyar NATO za ta dauki nauyin ba da horo da bada shawara da taimakawa kasar.

Babban jami'in NATO Anders Fogh Rasmussen ya nanata a gun taron koli cewa, kungiyar ba ta son sa baki kan rikicin kasar Sham, a halin yanzu, hanyar da ta fi kyau wajen kawo karshen wannan rikici ita ce gudanar da shirin shimfida zaman lafiya da manzon musamman na MDD da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa Kofi Annan ya gabatar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China