in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NATO ta zayyana ayyukan da za ta yi a Afghanistan yayin taron kolinta na Wales
2014-09-05 10:11:23 cri

Shugabannin kasashen kungiyar tsaro ta NATO 28 da kawayenta (ISAF) sun amince su kaddamar da wata sabuwar tawagar da ba ta yaki ba a kasar Afghanistan bayan shekarar 2014 da nufin taimakawa wajen horaswa, samar da shawarwari ga dakarun tsaron kasar ta Afghanistan.

Babban sakataren kungiyar ta NATO Anders Fogh Rasmussen shi ne ya bayyana wannan shiri ga taron manema labarai ranar Alhamsi a taron kolin kungiyar na Wales, ya ce, a karshen shekara ta 2014 ne sojojin kawancen (ISAF) za su kammala aikinsu a kasar Afghanistan, kuma aikin sabuwar tawagar NATO a Afghanistan, shi ne taimakawa sojojin kasar, karfafa hadin gwiwa na zahiri da na siyasa na dogon lokaci da kasar ta Afghanistan.

Batun kafa tawagar dai ta biyo bayan sanya sannu kan yarjejeniyar tsaro ne da Amurka ta yi da kasar ta Afghanistan.

Taron na Wales ya samu halartar ministan tsaron Afghanistan Bismillah Khan Mohammadi, shugabanni daga kasashen tsakiyar Asiya, da kuma wakilai daga kawaye na MDD da kungiyar EU. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China