A wannan rana kuma, babban taron NATO dake gudana a Tallin, babban birnin kasar Estonia ya soma tattaunawa kan matsalar, inda wakilai kimanin 300 da suka fito daga kasashe mambobi 28 na kungiyar, da kasashen dake hulda da ita guda 13, da majalisar dokokin Turai da sauran hukumomi za su tattauna batutuwan da suka shafi yanayin da Gabas ta Tsakiya da arewacin Afrika suke ciki, da tsaron intanet da kuma shigar da kasar Georgia cikin kungiyar, da dai sauransu.
A lokacin taron, matasan da suka fito daga kasashen Estonia, Latvia, Jamus, Finland, Sweden, Norway sun yi zanga-zanga a taron, domin nuna adawa da ayyukan kungiyar NATO a karkashin shugabancin kasar Amurka. (Bilkisu)