Qamar Zaman Kaira ya ce, kwamitin tsaron kasar Pakistan ya yi maraba da abin da Hillary Clinton ta yi, kuma taron ya yanke shawarar sake bude wannan hanya. Ya ce, wannan abu zai yi amfani wajen sa kaimi ga shimfidar zaman lafiya a Afghanistan, amma, kwamitin ya yanke shawara cewa, ba za ta yarda ba idan NATO ta yi sufurin makaman kare-dangi ta hanyar ratsa Pakistan.
Hillary Clinton ta tabbatar da wannan labari a ran 3 ga wata. Kuma ta gamsu da rawar da Pakistan ta taka wajen yaki da ta'addanci, kuma ta jaddada cewa, Amurka za ta yi hadin kai da Pakistan don yaki da ta'addanci da goyon bayan Afghanistan wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare kuma da kara yin mu'ammala tsakaninsu a fannin cinikayya da zuba jari.
A wannan rana kuma, shugaban NATO Anders Rasmusen ya nuna maraba da shawarar da Pakistan ta yanke.(Amina)