in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NATO ta yi kira ga kasashen duniya da su kara matsin lamba ga kasar Syria
2012-10-10 14:50:45 cri
A ranar 9 ga wata a birnin Brussels na kasar Belgium, babban sakataren kungiyar tsaron NATO Anders Rasmusen ya yi kira ga kasashen duniya, da su kara yiwa gwamnatin kasar Syria matsin lamba don cimma daidaito kan shirin warware rikicin kasar ta hanyar lumana.

An kaddamar da taron ministocin tsaron kasashe na kwanaki biyu na kungiyar tsaron NATO a ranar 9 ga wata a birnin Brussels, a wannan rana kuma babban sakataren kungiyar Anders Rasmusen ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a cibiyar kungiyar cewa, kamata ya yi kwamitin sulhu na MDD ya umurci gwamnatin kasar Syria da ta tsagaita wuta, tare da shiga shawarwarin siyasa. Amma ya zuwa yanzu, kwamitin sulhu na MDD bai tsara wani kuduri kan yadda za a cimma wannan buri ba.

Daga nan sai Rasmusen ya ce, idan akwai bukata, kungiyar tsaron NATO za ta dauki duk matakan da suka wajaba don bada kariya ga kasar Turkiya, kasa membar kungiyar, amma kungiyar tana fatan bangarori daban daban dake cikin rikicin, za su kwantar da hankali don magance tsanantar rikicin dake tsakanin Turkiya da Syria.

Bayan da babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya gana da shugaban kasar Faransa François Hollande a birnin Paris a wannan rana, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, tsanantawar rikicin kasar Syria na jefa al'ummar kasar cikin mawuyacin halin. Don haka gudanar da shawarwarin siyasa hanya ce kadai da za a bi don warware rikicin, kana ya yi kira ga gwamnatin kasar Syria da ta tsagaita bude wuta bisa gefe daya kuma ba tare da bata lokaci ba.

Bisa kididdigar da MDD ta yi, tun daga lokacin barkewar rikicin kasar ta Syria wato cikin watan Maris na bara kawo yanzu, mutane a kalla dubu 20 sun rasa rayukansu, sanadiyyar musayar hare-hare tsakanin sojojin gwamnatin kasar da dakaru masu adawa da shugaba Bashar Al-Assad, yayin da wasu mutanen kimanin dubu 300 suka tsere zuwa kasashen Jordan, da Iraki, da Lebanon da kuma Turkiya a matsayin 'yan gudun hijira. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China