in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron koli na kungiyar SCO a Bishkek babban birnin kasar Kyrgyzstan
2013-09-13 20:50:17 cri
Yau Jumma'a ran 13 ga wata da yamma ne aka kammala taron koli karo na 13 na kungiyar hadin gwiwa ta birnin Shanghai wato SCO a Bishkek, babban birnin kasar Kyrgyzstan. Kuma an samu sakamako mai gamsuwa kan harkokin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da suka hada da harkokin siyasa, tattalin arziki, tsaro da kuma al'adu da dai sauransu.

A yayin wannan taro kuma, shugabannin kungiyar sun cimma ra'ayi daya kan ci gaba da karfafa matakan yaki da fataucin miyagun kwayoyi, sayarwar da makamai da kuma kungiyoyi 'yan ta'adda. Bugu da kari, ya kamata kungiyar SCO ta ba da taimako ga kasar Afghanistan don shimfida yanayin zaman karko da na zaman lafiya a kasar.

Ban da hadin gwiwar harkokin tsaro, a sa'i daya kuma, shugabannin kungiyar suna ganin cewa, ya kamata a karfafa hadin gwiwa kan fannonin tattalin arziki da kuma zuba jari. Bugu da kari, shugabannin kungiyar sun kuma yi musayar ra'ayi kan yanayin kasar Syria , batun kasar Iran da dai sauran manyan batuttuwan kasa da kasa da na shiyya shiyya.

Yayin taron manema labaran da aka yi bayan taron, shugaban kasar Kyrgyzstan ya bayyana cewa, an kammala taron tare da samun sakamako mai gamsuwa, an kuma samu ci gaba kan harkokin hadin gwiwar mambobin kasashen SCO.

Bugu da kari, a yayin taron manema labarai, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Cheng Guoping ya nuna cewa, Sin na farin ciki sosai game da sakamakon da aka samu a taron kolin wannan karo. Kuma ta wannan taro, mambobin kasashen kungiyar SCO sun sake sanar da aniyarsu wajen kiyaye yanayin tsaron yankin, inganta harkokin ci gaban yankin, ci gaba da kyautata dokokin kasa da kasa da kuma ciyar da harkokin zaman lafiyar kasa da kasa gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China