An yi taron koli a karo na 13 na kungiyar tattaunawar hadin kai ta birnin Shanghai wato SCO a yau Juma'a ran 13 ga wata a Bishkek babban birnin kasar kyrgyzstan, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugabannin sauran kasashe da suka halarci taron.
Jigon taro wanda Shugaban kasar kyrgyzstan Mr Atambayev ya jagoranta a wannan karo shi ne "nazarin matakai da za a dauka wajen zurfafa zumunci tsakanin mambobin kasashe da hadin gwiwa tsakaninsu", ban da haka, za a yi musayar ra'ayi da daidaita ra'ayoyinsu kan wasu manyan batutuwa kasa da kasa da na shiyya shiyya.
A lokacin taro yana sa ran Shugaba Xi zai ba da jawabi don bayyana ra'ayin kasar Sin kan yadda za a zurfafa zumunci tsakanin mambobin kasashe da yin hadin gwiwa mai yakini tsakaninsu.
Haka kuma, shugabannin kasashe mambobi za su sa hannu kan yarjejeniyar Bishkek tare kuma da zartas da wasu manyan batutuwa ciki hadda tsarin kara zumunci da hadin gwiwa tsakanin mambobin kasashe cikin dogon lokaci. Rahoton aikin babban sakataren kungiyar SCO, da rahoton ayyukan da aka yi a cikin shekara daya da ta gabata, ayyukan da majalisar yaki da ta'addanci ta yi a shekara da ta gabata da sauransu, sannan kuma da gabatar da sanarwar taron, da tabbatar da sa hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin mambobin kasashen SCO a fannin kimiyya da fasaha. (Amina)