in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gabatar da ra'ayoyi 4 game da kungiyar hada kai ta Shanghai
2013-09-13 20:48:24 cri
A yau Jumm'a 13 ga wata, an kira taron kwamitin shugabannin kasashe mambobin kungiyar hada kai ta Shanghai a Bishkeke, babban birnin Jamhuriyar Kyrkyzstan. Shugabannin kasashen Sin, Kharzakstan, Kyrkyzstan, Rasha, Tajikstan, da na Uzbekstan sun halarci taron.

A yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar da wani jawabi, inda ya gabatar da ra'ayoyi 4 kan yadda za a yi hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar hada kai ta Shanghai. Mr. Xi ya ce, da farko dai, yada ruhun Shanghai na amincewa da juna, moriyar juna, zama tare cikin lumana, rika yin shawarwari tsakaninsu kan batutuwa iri iri da girmama al'adu iri daban daban domin neman ci gaba tare. Sannan ya kamata kasashe mambobin kungiyar su yi kokari tare domin tabbatar da zaman lafiya a yankin da suke ciki. Bugu da kari, su yi kokarin yin hadin gwiwa za zai kawo sakamakon a-zo-a-gani. Daga karshe dai, ya kamata su kara yin musaya kan abubuwan da suke shafar rayuwar dan Adam ta yau da kullum, kuma tsakanin jama'a, kan yadda za a iya karfafa tushen al'umma ga kokarin bunkasa kungiyar hada kai ta Shanghai.

Lokacin da yake tabo batun Syria, Xi ya jaddada cewa, bangaren Sin na mai da hankali sosai kan halin da ake ciki a kasar Syria, kuma ya nuna goyon baya ga kungiyoyin kasa da kasa, da kasashen duniya da su yi kokarin tsagaita bude wuta, neman sulhu da yin shawarwarin kawo zaman lafiya. Sannan ya kirayi bangarori masu adawa da juna na Syria da su warware matsalar da suke fuskanta a siyasance. Haka kuma, shugaba Xi Jinping ya ce, bangaren Sin na nuna goyon baya ga shawarar da kasar Rasha ta gabatar, wato mika wa kungiyar kasa da kasa makamai masu guba na Syria, kan yadda za a iya lalata su a inuwar sa idon kasashen duniya. Mr. Xi ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari ba tare da kasala ba wajen warware matsalar Syria a siyance. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China