Dangane da haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau Laraba 4 ga wata cewa, ya zuwa yanzu, an kwashe sama da shekaru 3 ana ricikin kasar Syria, lamarin da ya sanya jama'ar kasar cikin yanayin tashin hankali. Don haka, abu mafi muhimmanci dake gaban gwamantin kasar Syria a halin yanzu, shi ne, a dakatar da hare-haren da kasar ke fama da shi cikin sauri, ci gaba da taron shawarwarin Geneva, fara gudanar da shirin mika mulki a kasar, don warware ricikin kasar ta hanyoyin siyasa cikin sauri. (Maryam)