in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kwashe dukkan sinadaran da za a iya kera makamai masu guba daga kasar Syria
2014-06-24 15:44:17 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta bayar da wata sanarwa a ranar Litinin 23 ga wata, inda ta ce, kasar Syria ta riga ta kawar da dukkan sinadaran da za a iya kera makamai masu guba daga kasar, wannan ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta cika alkawarinta.

Sanarwar ta jaddada cewa, an yi jigilar sinadarai kashi na karshe da ake fatan lalata su a wajen kasar a ranar 23 ga wata. Gwamnatin kasar Syria ta kammala wannan aiki ne a cikin mawuyacin hali mai hadari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China