Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya fada yayin taron manema labarai cewa, hanya daya tilo ta magance rikicin kasar komai muninsa, ita ce hanyar siyasa.
Hong ya ce, kamata ya yi gwamnatin Syria, jam'iyyun adawa da sauran masu ruwa da tsaki, da su sanya muradun kasar da jama'arta a gaban komai kana su kawo karshen fada da tashin hankalin da ke faruwa a kasar, su kuma mayar da hankali kan tattaunawar Geneva.
A ranar Laraba ne majalisar dokokin kasar ta Syria ta bayar da sanarwar cewa, shugaba al-Assad ya lashe kashi 88.7 cikin 100 na kuri'un da aka kada, lamarin da ya ba shi damar ci gaba da wa'adi na uku na tsawon shekaru 7 yana mulki.
Wannan shi ne karo na farko a tarihin kasar Syria da aka gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan takara da dama, matakin da 'yan adawa da ke ketare da kasashen yammaci da ke mara musu baya suka yi watsi da shi. (Ibrahim)