Gabatar da batun halin da Syria ke ciki ga kotun duniya ta hannun kwamitin sulhun MDD zai haifar da tabarbarewar halin da kasar ke ciki
A yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru, a yau Alhamis, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hong Lei ya bayyana cewa, game da batun kasar Syria, kamata ya yi kasashen duniya su tsaya kan tsayin warware matsalar kasar a siyasance. Idan an gabatar da batun halin da kasar ke ciki a gaban kotun duniya ta hannun kwamitin sulhu na MDD, yanayin al'amurran da kasar ke ciki zai tabarbare, kuma za a samu cikas wajen warware matsalar kasar, jama'ar kasar da kasashen dake shiyyar, su ne za su sha wahala, saboda haka babu wata dabara sai kasar Sin ta jefa kuri'ar nuna adawa da daftarin kudurin kwamitin sulhu game da batun Syria.
Hong Lei ya kara bayyana cewa, ya kamata kasashen duniya su ci gaba da kokarin cimma burin tsagaita bude wuta tare da dakatar da ayyukan nuna karfin tuwo a kasar ta Syria, da kuma sassauta yanayin da jama'ar kasar suka shiga, musamman ma ta hanyar shawarwari na Geneva don taimakawa sassan biyu na kasar Syria, wajen nemo wata hanyar da za ta dace da halin kasa, wacce kuma ke iya kulawa da moriyar bangarorin da abin ya shafa. (Bilkisu)