Sanarwar ta ce, Ban Ki-moon na jaddada adawarsa kan bangarorin dake gaba da juna su rika amfani da makamai kan fararen hula, hakan ya keta ra'ayin jin kai na duniya da dokokin hakkin bil'adam. Kuma ya nuna damuwarsa da bakin ciki kan yadda kasashen duniya suka kasa hadin kai domin kawo karshen rikicin Sham ko neman hukunta masu hannu kan wannan hari.
Jama'ar Sham na bukatar kawo karshen nuna karfin tuwo cikin gaggawa, da fatan ganin an kafa wata sabuwar Sham dake iyar biyan bukatunsu da ba su kariya.
Kafofin yada labaru na Sham sun ba da labaru cewa, a daren ranar 21 ga wata, yayin da ake wani taron gangamin yakin neman zabe a lardin Dar'ā dake kudancin Sham na magoya bayan shugaban Sham, Bashar Al-Assad, sun ci karo da luguden wuta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 20, tare da raunana wasu sama da goma.
Bisa jadawalin da majalisar dokokin Sham ta bayar, an ce, jama'ar dake kasar Sham za su fara kada kuri'ar zaben shugaban kasar a ranar 3 ga watan Yuni, yayin da jama'ar kasar dake zaune a kasashen waje za su iya kada kuri'a a ofisoshin jakadancin Sham dake kasashen waje a ranar 28 ga watan Mayu. Tuni da manyan jam'iyyun dake adawa da gwamnatin Sham biyu suka kaucewa wannan babban zaben kasar. (Fatima)