in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala jefa kuri'u a zaben shugaban kasar Syria
2014-06-04 15:35:56 cri

Rahotanni daga kasar Siriya na cewa yanzu haka an kammala jefa kuri'un zaben shugaban kasar, an kuma fara kidayar su.

Kamfanin dillancin labarun kasar ta Siriya ya rawaito shugaban hukumar zaben kasar yana cewa, an kawo karshen jefa kuri'un zaben a dukkan tashoshin kada kuri'u dake kasar, an kuma fara kidayar su nan take.

Ya zuwa yanzu ba a bayyana sakamakon zaben ba, amma bisa labarin da wani gidan telebijin mai yada shirye-shirye daga kasar Lebanon ya fitar, an ce yawan mutane da suka jefa kuri'u a zaben na wannan karo ya kai kimanin miliyan 10, adadin da ya kai kashi 63 cikin dari na daukacin mutanen da suka isa jefa kuri'u a kasar, wato miliyan 15.84 wanda gwamnatin kasar ta gabatar kafin zaben.

Kawo yanzu kuma dai ba a bayyana yaushe ne za a bayyana sakamakon zaben ba.

Wannan ne dai karon farko da 'yan takara uku suka shiga zaben shugaban kasar ta Siriya, 'yan takarar da su ka kunshi shugaban kasar na yanzu Bashar al-Assad, da mamba a majalisar dokokin kasar Maher Abdul-Hafiz Hajjar, da kuma wani minista a tsohuwar gwamnatin kasar Hassan al-Nuri. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China