Wata sanarwa da aka fitar ta shafin yanar gizon hukumar OPCWn a jiya Talata ranar27 ga wata, ta tabbatar da sace rukunin ma'aikatan nata dake aiki a Sham, koda yake dai babu wanda ya rasu sakamakon hakan, kuma su na daf da komawa ofishinsu bayan an sake su.
Ya zuwa yanzu dai ba a tantance da wadanda suka kai farmakin kan ma'aikatan ba.(Zainab)