Mr. Ban ya ce, ya zuwa yanzu, ricikin kasar Syria ya riga ya haddasa mutuwar mutane sama da dubu 150, kuma sama da rabin mutanen kasar sun rasa gidajensu, yawan 'yan gudun hijira da aka yi rajista ya kai kimanin miliyan 2.8.
Game da haka ne, Mr. Ban ya gabatar da manufofi shida ga gamayyar kasa da kasa da za su kai ga warware rikicin kasar Syria, da farko, ya ce, ya kamata a kawo karshen ricikin kasar, musamman ma hana shigar da makamai cikin kasar Syria, idan kwamitin sulhu na MDD ba zai iya cimma matsaya guda kan batun ba, ya kamata kasa da kasa su dauki matakai da kansu wajen hana jigilar makamai zuwa kasar Syria.
Sauran manufofin sun hada da, gamayyar kasa da kasa su dukufa wajen kiyaye jama'ar kasar Syria, daukar matakai wajen ciyar da yunkurin warware ricikin kasar gaba, kammala aikin lalata makamai masu guba cikin sauri da dai sauransu. (Maryam)