Kotun ta yankewa Badie da wasu sauran shugabannin kungiyar su 8 hukuncin daurin rai da rai ne, bayan da wata kotun ta yanke musu hukuncin kisa a watan Yunin da ya gabata. Baya ga wadannan jagorori na kungiyar ta 'yan uwa musulmi, kotun ta kuma yankewa wasu magoya bayan kungiyar su 6 hukuncin kisa.
Shi dai hukuncin baya, da waccan kotu ta yankewa wadannan shugabanni da magoyon bayan kungiyar 'yan uwa Musulmi a watan na Yuni, ya biyo bayan samun su da ta yi, da lafin jagorantar hare-hare, a wani wurin kusa da Masalacin lardin Giza a watan Yulin bara, kafin daga bisani a sauya hukuncin bisa shawarar shugaban addinin kasar.
Kotu mai hukunta manyan laifuffuka dake El Minya dai ta yankewa Mohamed Badie hukuncin kisa ne a watan Yunin da ya shude, bayan da ta tabbatar da zargin da aka yi masa na shirya kaddamar da hare-hare, da kisan 'yan sanda da dai sauransu.
Tun dai lokacin da rundunar sojan kasar Masar ta hambarar da Mohamed Morsi daga mukaminsa na shugabancin Masar a watan Yulin shekarar da ta gabata kawo yanzu, magoyon bayansa ke ci gaba da gudanar da zanga-zanga a sassan kasa akai akai. (Maryam)