Magoya bayan tsohon shugaban kasar, sun yi ta shirya zanga-zangar adawa da gwamnati a duk fadin kasar domin, bikin cika shekara guda da murkushe gungun magoya bayan tsohon shugaban kasar Muhammed Morsi da suka taru a dandalin Rabaa al-Adawiya da birnin Alkahira da kuma dandalin Nahda da ke Giza.
Daruruwan magoya bayan tsohon shugaban kasar ne dai suka rasa rayukansu tun lokacin da sojojin suka hambarar da Morsi a watan Yulin shekarar da ta gabata a lokacin da jami'an tsaro suka tarwatsa sansanoni biyu na masu zanga-zangar.
A halin da ake ciki ma'aikatar cikin gidan kasar ta dauki tsauraran matakai a duk fadin kasar domin hana zanga-zangar. (Suwaiba)