in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana kudurinta na taimaka wa Masar
2014-08-04 10:19:10 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana kudurin kasar Sin ta taimaka wa Masar a kokarin da take na samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kasar.

Mr Wang ya bayyana hakan ne yayin da ya gana da shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi a ranar Lahadi a lokacin da ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar ta Masar, inda ya mika sakon shugaba Xi Jinping na taya al-Sisi murnar zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasar Masar.

A cikin sakon, shugaba Xi ya sake nanata kudurin Sin na taimaka wa Masar a kokarin da take na samar da zaman lafiya da bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma inganta rayuwar jama'a ta yadda za a bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a fannnoni da dama.

Ministan Wang ya ce, ziyarar tasa bisa umarnin shugaba Xi, wata alama ce da ke nuna irin cikakken goyon baya da Sin ke baiwa sabuwar gwamnatin Masar da Misirawa baki daya da kuma kudurin Sin na bunkasa dangantakar moriyar juna da ke tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare shugaba Sisi, ya nuna yabo da sakon taya murnar da shugaba Xi ya aiko masa da kuma goyon bayan da Sin ke baiwa kasar ta Masar, Kasar Masar dai tana shirin aiwatar da wasu ayyuka ciki har da shiyyar tattalin arziki da hadin gwiwar cinikayya ta Suez, ayyukan da ake maraba da Sin da ta zuba jari a ciki. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China