in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Sisi ya gana da dan majalissar kasar Amurka
2014-08-18 14:36:32 cri
Shugaba Abdel Fattah Al-Sisi na Masar ya gana da dan majalissar kasar Amurka Darrel Issa a birin Alkahira, game da kudurin bunkasa ci gaba, da tsaro, da ma batutuwa masu alaka da kalubalen ayyukan ta'addanci a yankin.

Da yake karin haske game da alakar dake tsakanin kasar sa da Masar, Mr. Issa ya ce Masar kawa ce ta kud da kud ga Amurka, za ta kuma iya taka muhimmiyar rawa wajen dakile barazanar ta'addaci a yankin da take.

Game da tallafin da Amurka ke baiwa Masar kuwa, dan majalissar ya ce tuni aka ware kudi har dala miliyan 500 ga kasar, baya ga wasu dala biliyan daya da za a warewa Masar din a shekara mai zuwa. Lamarin da a cewarsa, ke shaida irin kyakkyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Kaza lika Issa ya ce dangantakar ayyukan soji tsakanin sassan biyu, za ta ci gaba da habaka a nan gaba, karkashin tsare-tsaren hadin gwiwa masu yawa.

Wannan dai ziyarar aiki da dan majalissar na Amurka ya kai Masar, ta baiwa bangarorin biyu damar tattaunawa gane da batutuwa da dama, ciki hadda al'amuran da suka shafi kasar Sham, da matsalar rashin tabbas a zirin Sinai, da kuma batun fataucin makamai daga kasar Libiya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China