in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dubban mutane sun halarci bikin jana'izar saurayi bakar fata da wani dan sanda ya harbe a kasar Amurka
2014-08-26 14:22:04 cri

Dubban jama'a ne suka yi cincirindo a wata majami'ar dake unguwar Ferguson ta garin Saint Louis na jihar Missourin kasar Amurka a jiya Litinin, domin halarta jana'izar Michael Brown, bakar fatar nan dan shekaru 18 a duniya, wanda wani dan sandan kasar farar fata ya harbe har lahira.

Jama'ar da suka halarci jana'izar matashin sun hada da Matin Luther King na 3, dan shahararren mai rajin kare hakkin jama'ar nan wato marigayi Matin Luther King, da iyalan Trayvon Martin, da Sean Bell, wadanda dukkansu matasa ne bakar fata, da 'yan sanda kasar Amurka suka harbe a baya, duk da cewa ba sa aikata wani laifi ba.

Ban da su kuma, fadar shugaban kasar Amurka ta White House ita ma ta tura wasu jami'ai 3 domin halartar Jana'izar.

A yammacin ranar 9 ga watan Agustar nan ne dai Michael Brown dake tare da abokinsa a wani titi, ya hadu da fushin dan sandan farar fata, wanda ya harbe shi har lahira. Aukuwar wannan ta'asa ta sa al'ummar unguwar Ferguson suka gudanar da zanga-zanga don nuna takaicinsu, lamarin da daga baya ya kai ga tsananta matuka, har ta kai an yi dauki ba dadi tsakanin al'umma da 'yan sanda.

Daga bisani kuma an gudanar da karin zanga-zanga a wurare daban daban a wasu sassan kasar kamarsu Washington, da New York, da Chicago.

A kuma kokarin ta na shawo kan yanayin da ake ciki, gwamnan jihar Missouri Jay Nixon ya sanar da kafa dokar-ta-baci a unguwar Ferguson a ranar 16 ga wata, kaza lika ya tura sojoji zuwa wurin don tabbatar da doka da oda.

A nasa bangaren, shugaban kasar Barack Obama ya yi alkawarin gudanar da bincike kan lamarin, tare da bayyace komai ba tare da rufa-rufa ba. Ya kuma yi kira ga jama'a da su kai zuciya nesa, yana mai cewa bai kamata 'yan sanda su yi amfani da karfin tuwo fiye da kima kan fararen hula ba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China