Shugaba Obama a lokacin taron manema labaru a wannan rana a fadar white house ya bayyana cewa, game da halin da ake ciki a kasar Iraki, Amurka ba ta da manufar tinkarar kungiyar ISIL, manufar da ke bukatar goyon bayan kasashen dake yankin.Ya ce yanzu haka ya riga ya tura sakataren harkokin wajen kasar John Kerry zuwa yankin gabas ta tsakiya don tattauna yadda za'a kafa kawancen yaki da kungiyoyin masu tsattauran ra'ayi.
Game da rikicin kasar Ukraine, shugaba Obama ya bayyana cewa, kasar sa ta Amurka ba za ta dauki matakan soja don warware rikicin ba, kuma za ta ci gaba da yin kira ga kasa da kasa da su kara yin matsin lamba ga kasar Rasha. Har ila yau Shugaba Obama ya sanar da cewa, zai gayyaci shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko zuwa fadar white house abin da zai zama ziyara ta farko da Poroshenko zai kai kasar Amurka tun darewar sa wannan kujerar ta shugaban kasar Ukraine. (Zainab)