Rahotanni na cewa, cikin abubuwan da za a gudanar yayin taron za su hada da bikin budewa,taron majalisar zartaswa karo na uku, dandalin tattaunawar taron, da kuma wasu nune-nune. Haka kuma, akwai taron shawarwari kan kasuwannin yawon shakatawa a taron koli na wannan karo, inda za a gayyaci wakilan kasashen da suke karbar masu yawon shakatawa daga kasar Sin da za su hada da kasashen Jamus, Faransa, Rasha, Japan, Koriya ta Kudu da wasu kasashe sama da 20 da ake sa ran za su halarci taron shawarwarin. (Maryam)