in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya karbi kyautar yabon yawon bude ido
2014-06-05 11:56:30 cri

Hukumar yawon bude ido da cinikayya ta kungiyar kasashen tarayyar Turai, wacce ke da babban ofishin a kasar Romania, ta baiwa shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe kyautar yabo ta gamsuwa da kasar Zimbabwe a fannin yawon bude ido.

A watan jiya ne, hukumar yawon bude idon ta baiwa Zimbabwe kyautar yabo ta shekara 2014 da kasar da ta fi ko wace kasa a duniya farin jini a zukatan masu yawon bude ido, Zimbabwen ta kuma zarce ko wace kasa ban sha'awa a wurin ziyara saboda al'adunta na gargajia.

Hukumar ta kuma baiwa ministan yawon bude ido na Zimbabwe Walter Mzembi digirin yabo, an kuma ba shi mamba na hukumar yawon bude ido na Turai.

Shugaban hukumar yawon bude ido mai hedkwata a Romania, Antron Caragea ya ce, kyautar yabo da aka baiwa Zimbabwe, an ba da ita ce domin yabawa kokarin da kasar take yi wajen bunkasa yawon shakatawa da kare muhalli da tarihi da kuma al'adu.

A yayin da yake jawabi bayan ya karbi kyautar yabon, shugaba Mugabe ya ce, zaben Zimbabwe da aka yi ya yi nuni da zarce kasashe da kasar ta yi na albarkar kayayyakin da ake shaidawa masu yawon bude ido wanda babu kamar su. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China