A halin da ake ciki, hankula sun fara kwantawa a sassan kasar Mali daban daban, bayan da aka bayyana tsohon firaministan kasar Ibrahim Boubakar Keita a matsayin mutumin da ya lashe zagaye na biyu na babban zaben kasar da ya gudana a karshen makon jiya.
A tsibirin Mopti, dake tsakiyar kasar, hankulan al'umma sun fara kwantawa, bayan aukuwar rikicin watan Janairun da ya gabata, wanda ya ritsa da yankin. Wani matashi mazaunin tsibirin na Mopti mai suna Hamidou Guindo, ya bayyanawa kanfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua, yadda a watan na Janairu, magoya bayan kungiyar 'yan tawayen Islama suka mamaye garin Konna, mai nisan kilomita 55 daga arewacin Mopti, kafin daga bisani dakarun hadin gwiwar kasa da kasa su fatattake su.
Guindo ya ce, aukuwar wannan lamari ya haifar da koma baya mai yawa ga harkar 'yan yawon shakatawa, baya ga rashin aikin yi da masu yiwa 'yan yawon shakatawar jagora irinsa suke fuskanta. Bugu da kari matashin ya ce, garin na Mopti wuri ne da masu gudanar da ayyukan ibada na gargaji, daga sassan kasar ta Mali ke halarta a kowace shekara, sai dai zaman dar dar da aka shiga ya sanya mutane kaurace halartar yankin.
Sassa daban daban a kasar Mali dai sun shiga wani mawuyacin hali na karancin tsaro a bara, sakamakon fadace-fadacen kabilanci, da tawayen da kabilun Larabawa da na Buzaye ke yi musamman a arewacin kasar, sakamakon mai da su saniyar ware da suke zargin kabilun kudanci kasar. (Saminu)