Jimillar kudi da kasashen dake kudu da Sahara suka samu a fannin yawon shakatawa ta kai dala biliyan 36 a bara
Kwanan baya, bankin duniya ya ba da sabon rahoton cewa, a shekarar 2012, baki daya masu yawon shakatawa miliyan 33.8 ne suka je yankin Afirka dake kudu da hamadar Sahara. Matsalar tattalin arzikin da kasashen duniya ke fama da ita ba ta yi illa sosai ga sha'anin yawon shakatawa a yankin ba, shi ya sa jimillar kudi da aka samu a wannan fanni ya kai dalar Amurka biliyan 36, wadda ta kai kashi 2.8 cikin dari bisa yawan GDP da aka samu a wannan yanki.
Bugu da kari, rahoton ya kara da cewa, ya kamata ne kasashen Afirka su kyautata kayayyakin yawon shakatawa irin na gargajiya idan suna son kara bunkasa sha'anin yawon shakatawa, wato ni'imtattun wurare na al'adun bil'adam, da mutane masu zumunci ba za su isa ba.(Fatima)