Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe da takwaransa na kasar Zambia Michael Chilufya Sata da babban sakataren kungiyar kula da harkokin yawon shakatawa ta duniya Taleb Rifai da ma baki sama da dubu da suka zo daga kasashe mambobin kungiyar sun halarci bikin bude taron.
A jawabin da ya yi a gun bikin bude taron, shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya ce, harkar yawon shakatawa na da muhimmanci ga bunkasuwar harkokin siyasa da tattalin arziki, kuma ba kawai ga Zimbabwe da Zambia ba, abin haka yake ga kasashen Afirka baki daya.
A shekarun baya, a yayin da tattalin arzikin duniya ke tabarbarewa, harkar yawon shakatawa ta tabbatar da saurin bunkasuwa a duniya, musamman a nahiyar Afirka. kididdigar da aka yi ta nuna cewa, a farkon rabin wannan shekara, yawan kudin da aka samu ta harkar yawon shakatawa a Afirka ya karu da kashi 5% bisa na makamancin lokacin bara, wanda ya zarce kashi 3% da 4% a hasashen kungiyar kula da harkokin yawon shakatawa ta duniya. Duk da haka, adadin ya dau kashi 4% kawai na yawan kudin da aka samu daga harkar yawon shakatawa a duniya baki daya, kuma rashin karfin tallata harkokin yawon shakatawa da koma bayan na'urori suna yi wa harkar tarnaki.
Kungiyar kula da harkokin yawon shakatawa ta duniya ta kan kira taronta a shekaru biyu biyu, taron da ya kasance mafi kasaita ta fannin harkar shakatawa. Zimbabwe da Zambia wadanda suke mallakar babbar mafadar ruwa ta Victoria tare suka shirya taron na wannan shekara cikin hadin gwiwa, hakan nan ya zama karo na farko da aka shirya taron a kudancin nahiyar Afirka.
A gun taron, za a tattauna batun makomar harkokin yawon shakatawa a duniya da bunkasa yawon shakatawa a Afirka, kuma za a shirya jerin harkokin talla a yayin taron. za a rufe taron a ranar 28 ga wata a birnin Livingston na kasar Zambia. (Lubabatu)