in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan shakatawa ya samar da ayyukan yi a jihar Xinjiang ta kasar Sin
2014-02-10 15:29:06 cri

Karuwan masu yawon shakatawa ya haifar da yawan ayyukan yi a jihar Xinjiang Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin a shekarar bara, in ji mahukuntar kasar.

A bisa kididdigar da hukumar kula da aikin yawon shakatawa ta jihar ta yi, an nuna cewa, fiye da sabbin ayyuka miliyan 1.5 aka samar sakamakon mai da hankali da mahukuntar jihar suka yi a bangaren yawon shakatawa da suka hada da masaukan baki da shagon sayar da kayayyakin kyututtuka.

Jami'an hukumar sun yi bayanin cewa, gwamnatin jihar ta Xinjiang ta fitar da kudi Renminbi yuan million 12, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 1.96 domin gina wuraren shan iska guda uku, gyara kauyuka 32 da garuruwa da unguwoyi, har ma da masaukan baki na gidaje 149 a shekarar bara.

A lokacin bikin bazarar da aka kwashe mako daya, ana yi tsakanin ranar 31 ga watan Janairu zuwa ranar 6 ga watan Fabrairu na bana kawai, an samu masu yawon shakatawan daga sauran wuraren gidan kasar Sin da suka kai kusan miliyan daya a jihar, sannan sun kashe kudin Sin yuan miliyan 739 wanda ya zarce na shekarar bara da kashi 20 a cikin 100.

Ni'imtattun wuraren shakatawa na Xinjiang da al'adunta na musmaman sun jawo jama'a fiye da miliyan 52 daga gida da kasashen waje a shekarar bara ta 2013, adadin da ya nuna karuwa fiye da kashi 17 a cikin 100 idan aka kwatanta shi da na makamancin lokaci na shekarar 2012. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China