Bugu da kari, asitibin jami'ar Emory ta kasar Amurka ya bayyana a ran 21 ga wata cewa, bayan jinya ta makwanni biyu da aka baiwa Amurkawan nan biyu da suka kamu da cutar Ebola a asibitin, ya zuwa yanzu, sun warke. Sa'an nan kuma, cibiyar yin rigakafi da kuma hana yaduwar cututtuka ta kasar ta sanar da cewa, a halin yanzu, babu kwayoyin cutar Ebola a jikinsu, wannan ya sa ba za su kawo barazana ga lafiyar sauran mutane ba, don haka ba za a takaita zirga-zirgarsu ba. (Maryam)