in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa ta bukaci da a kira taron gaggawa na kwamitin tsaro kan Iraki
2014-08-08 10:16:34 cri
Kasar Faransa na nuna damuwa sosai kan yadda mayakan daular Musulunci a Iraki da Levant (EIIL) suke ci gaba da mamaye arewacin Iraki, tare da bayyana fatanta na ganin an kira taron gaggawa na kwamitin tsaro na MDD, in ji ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius a ranar Alhamis a cikin wata sanarwa.

Faransa na nuna damuwa sosai kan yadda EIIL take mamaye arewacin Iraki tare da kwace Qaraqosh, birnin dake kunshe da al'ummar Kiristoci mafi girma a Iraki tare kuma da aikata munanan ayyuka kan al'ummar wuraren, in ji mista Fabius.

Game da tsanancewar halin da ake ciki musamman ma dake shafar fararen hula da mabiya kananan addinai, Faransa na bukatar da a kira taron gaggawa na kwamitin tsaro domin ganin gamayyar kasa da kasa ta mai da hankali domin yaki da barazanar ta'addanci a kasar Iraki da kuma ba da taimako da kariya ga al'ummomin kasar Iraki dake fuskantar barazana, in ji shugaban diplomasiyyar kasar Faransa. A ranar Laraba a yayin wata hira ta wayar tarho, shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya nuna damuwarsa ga sarkin Jordaniya game da kafuwar kungiyoyin ta'addanci na daular musulunci a Siriya da Iraki dake takurawa mabiya kananan addinai, in ji fadar Elysee a cikin wata sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China