Wata sanarwa wacce kakkakin MDD ya gabatar ta ce yawancin wadanda suka rasa muhallan sun fito ne daga al'ummar Yezidi, Ban ya yi kira da babbar murya da a tabbatar da tsaron lafiyar jama'ar da suka rasa muhallansu, ya kuma yi gargadi cewar duk wani harin da za'a kai a kan wani bangaren farar hula saboda dalilai na kabila ko addini zai zamanto aikata laifi ga bil'adama, kuma wadanda aka kama da aikata hakan dole su dauki nauyin aikata irin wannan laifi.
Ban ki-moon ya nuna takaicin sannan ya yi kira a kan gwamnatin Iraq da gwamnatin shiyya ta Kurdistan da su aje banbancinsu a gefe guda tare da gudanar da aiki tare domin magance matsalar tsaro dake addabar kasar tare da tabbatar da tsaron lafiyar fararen hular dake yankunansu da kuma tabbatar da kariyar 'yancin kasar ta Iraqi.
Babban sakataren ya yi kira a kan dokacin 'yan Iraqi da su taimakawa wadanda suka rasa muhallansu, sannan kuma ya tunatar da duk bangarorin dake fada da juna da su kwana da sanin nauyin da ya rataya a wuyansu na baiwa kungiyoyin agaji damar shigowa kasar domin taimakawa wadanda suke gujewa tashin hankalin da ya barke a kasar. (Suwaiba)