in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Iraki sun gana da manzon musamman na kasar Sin mai kula da batun yankin Gabas ta Tsakiya
2014-07-09 10:53:04 cri

Mataimakin firaministan kasar Iraki Saleh al-Mutlaq da ministan harkokin wajen kasar Hoshyar Zebari sun gana da Wu Sike, manzon musamman na kasar Sin mai kula da batun yankin Gabas ta Tsakiya a ranar Litinin 7 ga wata a birnin Bagadaza, hedkwatar kasar.

A yayin ganawar, al-Mutlaq ya gode wa mista Wu da ya ziyarci kasarsa a yayin da Iraki take cikin mawuyancin hali, ya kuma bayyana cewa, Iraki na himmantuwa wajen sa kaimi kan samun sulhuntawa ta fuskar siyasa, ya kuma yi imani da cewa, za a kafa sabuwar gwamnati cikin hanzari. Al-Mutlaq ya kara da cewa, Iraki na dora muhimmanci kan tasirin da kasar Sin take yi a al'amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya, tare da yabawa babbar gudummowar da Sin ke bayarwa a fannin sake gina Iraki. Iraki na son ci gaba da inganta hadin gwiwa a tsakaninta da Sin a sassa daban daban.

A nasa bangaren, Wu Sike ya ce, kasar Sin na goyon bayan kokarin da Iraki take yi wajen tabbatar da kwanciyar hankali da yaki da ta'addanci da sauran fannoni. Sin ta yi imani da cewa, sassa daban daban na Iraki za su inganta hadin gwiwa wajen kafa gwamnati da za ta mai sulhunta al'ummar kasar cikin hanzari.

Har wa yau a yayin da yake ganawa da mista Wu, ministan harkokin wajen kasar ta Iraki Hoshyar Zebari ya gode wa kasar Sin da ta goyi bayan kokarin da Iraki ke yi wajen yaki da ta'addanci da tabbatar da kwanciyar hankali. Ya kuma yaba wa kasar Sin da ta goyi bayan shirin Iraki ta fuskar siyasa da farfado da tattalin arzikin kasar, da kuma yadda ktake taimakawa Iraki a wadannan fannoni. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China