Wani turmutsutsu ya janyo hasarar rayukan mutane 24 a birnin Konakiri na kasar Guinea.
Rahotanni daga kasar sun nuna cewa, an tattake mutane da dama a jiya Talata, a kusa da wani yanki dake bakin tekun kasar, lokacin da wata shahararriyar kungiyar mawakan kasar ke cashewa domin bikin karamar sallah.
Tuni dai gwamnatin kasar ta sanar da zaman makoki na mako guda, domin nuna alhinin faruwar wannan tsautsayi. (Amina)