Wata sanarwar kakakin sakataren janar na majalisar dinkin duniya, ta yi kira a kan hukumomi da jama'ar Guinea-Bissau, su tabbatar da an gudanar da karbabben zaben a cikin kwanciyar hankali gobe Lahadi.
Sanarwar ta ce tun da hannu daya baya daukar jinka, ya kamata wadanda za su yi takara da magoya bayansu, da kuma gwamnatin rikon mulkin kasar, da hukumomi masu gudanar da zabe, da kungiyoyi kare hakkin jama'a da gabadayan jama'a su fahimta cewar suna da rawar da za su taka domin haka ta cimma ruwa.
Sanarwar ta yi hasashen cewar, samun nasarar gudanar da zaben zai agaza wajen maido da doka da oda a kasar ta Guinea Bissau, kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada, hakazalika za'a samu bunkasar tafiyar da al'amurra kamar yadda dokar kasa ta zayyana.
Sanarwar ta kara da cewar nasarar zaben zai iya maido da taimakon agaji da kasashen duniya ke baiwa kasar, wanda a halin yanzu aka dakatar. Sanarwar kakakin sakatare janar din na majalisar ta dinkin duniya ta ci gaba da cewa aiwatar da zabe na gaskiya a Guinea Bissau, wani abu ne da ka iya share hanya na samun dorewar zaman lafiya na siyasa tare da aiwatar da shirukka na tsawon lokuta domin dasa tushen zaman lafiya tare da zaburar da gina kasa da habbakar tattalin arziki tare da goyon bayan kasashen waje. (Suwaiba)