Ya zuwa ranar 28 ga watan Afrilu gwamnatin kasar Guninea da abokan huldarta ciki har da kungiyar lafiya ta duniya da kungiyar likitoci ta Na gari na kowa(MSF) sun tabbatar da cewa,mutane 121 ne suka kamu da cutar zazzabin Ebola a kasar,ciki har da mutane 74 da suka mutu a cibiyoyin kula da marasa lafiya daban-daban da suka kafa.
Kididdigar da ma'aikatar lafiya ta kasar ta bayar a ranar Talata, ta nuna cewa,an kwantar da mutane da 10 a asibiti a halin yanzu sanadiyar cutar,guda 4 a garin Conakry kana 6 a kudu maso gabashin garin Guekedou . (Ibrahim)