in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nuna kyakkyawan fata ga kudurin tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Falesdinu
2014-07-23 10:35:28 cri

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, wanda a halin yanzu ke ziyarar aiki a Gabas ta Tsakiya ya bayyana cewa, yana fata da kyakkyawan zaton cimma burin tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Falesdinu.

Mr. Ban wanda ya bayyana hakan ne a ranar Talata 22 ga watan nan, ya yin da yake gabatar wa kwamitin sulhu na MDD yanayin da ake ciki a zirin Gaza ta bidiyo daga birnin Ramallah dake yammacin kogin Jordan.

Babban magatakardan MDD wanda ya ce, ya yi shawarwari masu ma'ana da shugabannin yankin a ziyarar aikin da ya gudanar a wannan karo, ya ce an samu sakamako mai gamsarwa game da hakan, ko da yake dai bai yi cikakken bayani game da shawarwarin da suka gudanar, don gane da yanayin da yankin ke ciki a halin yanzu ba.

Mr. Ban ya jaddada cewa, abubuwa uku da suka fi muhimmanci a halin yanzu, a fannin warware rikicin Isra'ila da Falescinu su ne, tsagaita musayar wuta ba tare da bata lokaci ba, da gaggauta hawan teburin shawarwari, da kuma warware tushen rikicin.

Ya ce idan har aka gaza warware tushen rikicin, to ko shakka babu ba za a iya kawo karshensa ba. Bugu da kari Mr. Ban ya ce kamata ya yi a yi amfani da kudurin da kasar Masar ta gabatar na tsagaita bude wuta.

Mr. Ban ya kai ziyarar aiki a Isra'ila a dai wannan rana, a kokarinsa na janyo hankalin Isra'ila ta kai zuciya nesa, tare da dakatar da daukar matakan soji a zarin Gaza. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China