A cikin sanarwar da aka gabatar a wannan rana, babbar jami'ar harkokin hakkin bil'adam ta MDD, madam Navanethem Pillay ta nuna damuwarta sosai kan cewa, Palestinu da Isra'ila na nuna wa junansu karfin tuwo, kuma hakan ya janyo mutuwar mutane da kawo illa ga zaman lafiya da rashin amincewa da juna, abin da ya kara tsananta rikicin.
Madam Pillay ta jaddada cewa, kowane irin matakan soja, bai kamata ya kawo illa ga fararen hula ba, kuma bai kamata a kai hari ga muhallinsu ba. Jami'ar ta yi allawadai da hare-haren da suka haddasa mutuwa da jikkatar fararen hula, ciki har da kananan yara da mata, tare da yin kira ga bangarorin biyu da su tsagaita bude wuta nan take, domin daidaita wannan matsala cikin lumana.(Fatima)